Tsohon gwamnan jihar Neja, Dr. Mu'azu Babangida Aliyu, ya ce akwai yiwuwar ya maka gwamnatin Najeriya a kotu saboda sanya sunansa a cikin jerin sunayen wadanda ake zargi da wawure dukiyar kasar.
A firar da ya yi da Muryar Amurka Dr Muazu Babangida Aliyu ya ce ya yi mamakin ganin sunansa a cikin jerin sunayen wadanda ake zargi da wawushe dukiyar kasa domin kuwa shi ko kwandala ba'a bashi ba.
Ita dai gwamnatin Najeriya ta ce Dr Babangida Aliyu ya yi sama da fadi da Naira miliyan dubu daya da miliyan dari shida.
A cewwarsa "Da muka yi taron kafa sabuwar PDP mu bakwai ne. Mutane biyar suka canza sheka zuwa APC amma ni da Sule Lamido muka ci gaba da PDP. Sabo dahaka sauran manyan jami'iyyar PDP basu yadda damu ba. Da suka tashi raba kudin kemfen ba'a bamu komi ba sai ji na keyi".Injishi wadanda suka karbi kudin a jihar Neja daga baya ya ji.
Dr Babangida Aliyu ya ce zasu rubuta wa ministan labarai Lai Muhammad da hukumar EFCC dake bincike su kawo shaidar cewa an bashi kudi idan ba haka ba kuma ya sheka kotu.
Amma tsohon gwamnan na fuskantar wasu tuhume-tuhume akan zargin yin sama da fadi da wasu kudaden jihar kodayake ya ce wannan bai sa gabansa ya fadi ba.
Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari da karin bayani
Facebook Forum