Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Sun Gano Gawarwaki 9 A Cikin Wani Jirgin Ruwa A Gabar Tekun Brazil


Brazil, Afrilu 15, 2024
Brazil, Afrilu 15, 2024

'Yan sandan kasar Brazil da ke bincike kan gano wani karamin jirgin ruwa cike da gawarwaki sun ce akwai yiwuwar gawarwakin na 'yan ci-rani ne daga kasashen Mali da Mauritania a nahiyar Afrika.

WASHINGTON, D. C. - A ranar Asabar ne masunta a jihar Pará da ke gabar teku a arewacin Brazil suka gano karamin jirgin ruwan a kan tekun Atlantika. Rundunar ‘yan sandan tarayyar ta Brazil ta fada a cikin wata sanarwa da ta fitar a yammacin Litinin cewa ta gano gawarwakin mutane tara.

Sanarwar ta ce "Takardu da wasu abubuwa da aka gano a kusa da gawarwakin sun nuna cewa wadanda abin ya shafa 'yan ci-rani ne daga nahiyar Afirka, kuma daga yankin Mauritania da Mali." 'Yan sandan sun kara da cewa ta yiwu akwai ‘yan wasu kasashe a cikin wadanda suka mutu.

Karamin jirgin ruwan mai tsawon mita 12, mai launin fari da shudi da aka kera kamar kwale-kwale wanda aka gano a Brazil, yayi kama da irin na masu kamun kifi a kasar Mauritaniya wanda bakin haure da ‘yan gudun hijira ke yawan amfani da shi a yammacin Afirka don tserewa zuwa tsibirin Canary na Spain, abin da ke nuni da yiwuwar ba Brazil ce ainihin kasar da suka yi niyyar zuwa ba.

Hanyar jirgin ruwa ta tekun Atlantika daga yammacin Afirka zuwa yankin Tarayyar Turai na daya daga cikin hanyoyin ruwa mafi hadari a duniya. Kananan jiragen ruwa da basu iya kai wa inda zasu ba, igiyar ruwa na iya kaisu yamma daga gabas, su kwashe watannin a kan ruwa. Baƙin da ke cikin irin wadannan jiragen galibi suna mutuwa saboda kishin ruwa da rashin abinci mai gina jiki. Wasu kuma suna iya fadawa cikin tekun saboda takaici.

Wani bincike da kamfanin dillancin labarai na Associated Press ya wallafa a bara, ya nuna cewa a shekarar 2021, an gano akalla jiragen ruwa bakwai daga arewa maso yammacin Afirka a yankin Karebiya da Brazil, dukkansu dauke da gawarwaki.

-AP

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG