Wadan da abin ya shafa na baya bayan nan, ‘yan sanda sun ce an harbe shi ne a daren Jumma’a da ta wuce, a wani kisa da shugabannin addinin Isalama na yankin suka ce ya faru ne jim kadan bayan ya halarci jana’izar wasu mutane biyu da aka kashe a cikin makonnin biyu da suka gabata.
‘Yan sanda sun ce dukkannin wadannan mutane uku, da kuma wanda aka kashe na farko da aka harbe a watan Nuwambarn bara, maza ne Musulmai ‘yan asalin kasar Pakistan ko kuma Afghanistan da ke zaune a Albuquerque, birnin mafi girma a jihar.
‘Yan sanda sun bada yan bayanai kadan kan kisan na baya bayan nan, amma sun bayyana kisan na farko guda uku da harbe-harben kwanton bauna.
Gwamna Michelle Lujan Grisham ta bayyana su a matsayin kashe-kashen da aka auna Musulmi mazauna yankin.
Shugaban Amurka Joe Biden ya wallafa a shafinsa na twitter a ranar Lahadi yana nuna goyon bayansa ga al’ummar Musulmi, ya kuma kara da cewa, wadannan hare-haren nuna kyama ba abin lamunta ba ne a Amurka.
Jami’an ‘yan sandan Albuquerque sun shaidawa manema labarai sa’o;’I bayan aukuwar lamarin cewa, suna bin diddigin wasu bayanai tare da fitar da wata sanarwa mai dauke da hotunan mota kirar Volkswagen mai kofa hudu, da ke da launin ruwan toka mai duhu da ke da bakin gilashi, wadda suka bayyana a matsayin motar da ake nema a binciken.
Sai dai ba’a san yadda motar ke da alaka da lamarin ba, kuma ‘yan sanda sun ce har yanzu basu tantance ko suna neman mutum daya ko fiye da haka a binciken ba.