Buda-bakin da ya gudana a karshen mako a karamin ofishin jakadancin da ke birnin Ikko, ya gudana ne a karkashin babbab jami'in diflomasiyyar Amurka da ke Lagos, Mr. David Greene, kamar yadda sanarwar ta nuna, shi wannan buda baki dai an shirya shine albarkacin azumin watan Ramadan.
Rukunan jama'a dai daban daban ne suka halarta wannan bikin buda baki, ciki har da ‘yan kasuwa, ‘yan jaridu, masu ruwa da tsaki a fannin fasaha, malamai da abokan Amurka, ana kuma son cimma kara jaddada akidar Amurka na yin hakuri da juna a sha'anin addini da kuma ‘yanci.
Mai sharhi kan al'amuran diflomasiyya, Bashir Danmusa, ya ce wannan bude- baki da Amurkan ta shirya babban abin a yaba ne domin hakan zai kara karfafa alakar zumunci da fahimtar juna.
Ya ce duk wanda zai gayyaceka walima ba karamin karramaka yai ba, musamman a irin wannan lokaci da ake fafutikar kara alaka duba da matsayin Amurka na babbar kasa a duniya.
Saurari cikakken rahoton Hassan Maina Kaina: