Kungiyoyin fafutukar wayar da kan ‘yan kasa, tabbatar da zaman lafiya da kuma neman adalci wajen kula da muhalli da suka hada da CEPEJ, CDE da kuma AFP wato Africa for Peace a turance sun yi wannan kira ne a wani taro da ya gudana a birnin tarayya Abuja suna masu cewa, kamata ya yi dukkan wadanda basu ji dadin yadda aka gudanar da zabe da bayyana sakamakonsa ba, su bi hanyoyin da suka dace na shari’a wajen mika koke da neman a bi musu hakinsu ba wai yin kalamai da ka iya tada rikicin kabilanci, addinni da kuma bangaranci a Najeriya ba.
Wannan kira dai na zuwa ne a daidai wata gabar da wasu mutane ke yin kiraye-kiraye a kan kar a yarda a kafa sabuwar gwamnati ko rantsar da zababben shugaban kasa da maitaimakinsa da kuma batun kafa gwamnatin rikon kwarya kafin a kamalla aikin sauraron korafe-korafen da 'yan takarar jam’iyyun adawa na Leba, PDP da dai sauransu suka shigar a gaban kotu na cewa an tafka magudi a zaben shugaban kasa da ya gudana a watan Febrairu, wasu kuma na shelar cewa, su suka lashe zabe an yi amfani da karfin mulki ne wajen kwace musu nasara.
A hirar ta da Muryar Amurka, Farida Sani Kambra, mamba a kungiyar mata masu ilimi a fanonnin rayuwa daban-daban ta Najeriya reshen jihar Kano ta bayyana cewa Najeriya ta fi karfin kowanne mutum daya kuma kasar da zaman lafiyarta ce a gaban su a matsayin kungiya.
Ambassada Ibrahim Waiya daya ne daga cikin jagororin kungiyoyin da suka shirya taron fadakar da ‘yan Najeriya da su yi hakuri su gujewa sauraron wasu ‘yan siyasa da suke fifita bukatunsu a kan na 'yan kasar yana mai cewa, abu mafi dacewa shi ne a rungumi zaman lafiya, hadin kan kasa da kuma tabbatar da an mika mulki cikin ruwan sanyi a watan Mayun mai zuwa.
A wani bangare kuma Kwamared Mulada Sherrif dake zaman jagoran cibiyar tabbatar da zaman lafiya da neman adalci wajen kula da muhalli wato CEPEJ cewa ya yi ganin yadda wannan shi ne karo na bawai da ake gudanar da manyan zabuka a Najeriya kuma ba zai zama na karshe ba, baya ga cewa an riga an wuce babin gudanar da zaben wannan shekara, a matsayinsu ‘yan Najeriya kamata ya yi su rungumi zaman lafiya saboda ranar 29 ga watan Mayun mai zuwa na da mahimmacin gaske yana mai yin kira ga yan takara da suka fadi zabe da su ci gaba da bin kadunsu a kotu su kuma yi kira ga magoya bayansu da su mutunta yarjejeniyar zaman lafiya na kwamitin NPC da jam’iyyun suka rattaba hannu a kai a watan Febrairu don gudun tada fitina a kasa saboda Najeriya zata ci gaba da zama a matsayin kasa mai cikakken iki bayan watan Mayun.
Idan Ana iya tunawa dai, an gudanar da babban zabe da ya samar da sabon shugaban kasa da mataimakinsa da kuma 'yan Majalisun Tarayya a Najeriya ne a ranar 25 ga watan Fabrairun shekarar 2023 karkashin shugaba Muhammadu Buhari, wanda ke karasa wa’adin mulkinsa karo na 2, zaben da ake kallo a matsayin takarar da aka yi goggaya mafi karfi tsakanin jam’iyyu fiye da biyu tun bayan kawo karshen mulkin soja a shekarar 1999.
A saurari cikakken rahoton Halima Abdul-Ra'uf: