Bayan wani hasashe da tsohon shugaban hukumar zaben Najeriya, Farfesa Attahiru Jega ya yi wanda ya fadi cewa wasu shugabannin kwamitocin Majalisa na amfani da matsayinsu wajen karbar na goro daga shugabannin hukumomi da aka dora musu alhakin sa ido a ayyukansu.
Sai dai Farfesa Jega bai fadi sunayen ‘yan Majalisar da yake magana akansu ba, ko kuma lokacin da aka yi hakan.
Furucin Jega dai ya janyo martanin Majalisar inda shugabanta Bukola Saraki ya bukaci idan har hakan ya faru, a taimaka musu a gabatar da sunayen wadanda suka yi hakan.
Mai magana da yawun Majalisar Dattawa Sanata Aliyu Sabbi Abdullahi, ya ce dalilin da ya sa Majalisa bata ji dadin wannan furuci ba shi ne, maganar na nuni da cewa ana gudanar da cin hanci da rashawa a baki dayan Majalisar.
Shi kuma Sanata Ali Ndume ya yi nuni da cewa ba duka aka taru aka zama ‘daya ba a Majalisa, kuma yin wannan furuci ba a kyautawa ‘yan Majalisun da ba su da irin wannan hali ba.
Facebook Forum