Wani rahoto da hukumomin tsaron Najeriya suka gabatar wa shugaba Muhammadu Buhari, ya yi nuni da cewa ‘yan kungiyar IS reshen yammcin Afirka ISWA ne suka kai wasu hare-haren da suka auku a wasu sassan kasar a ‘yan kwanakin nan.
Daga cikin hukumomin tsaron da suka tabbatar da hakan, har da hukumar tsaro ta farin kaya, wato SSS.
Mutane da dama ne suka rasa rayukansu a sassan Najeriya, musamman a tsakiyar arewacin kasar.
Jihohin Benue da Taraba na daga cikin inda aka yi wadannan kashe-kashen, wadanda ake dangantawa da rikicin manoma da makiyaya.
A makon da ya gabata hukumomin tsaro sun cafke mahara da dama wadanda ake zargin su da kai wadannan hare-hare.
Daga cikin wadanda aka kama akwai mayakan Fulani da mayaka na sa-kai da gwamnati ke marawa baya da kuma sauran tsageru masu ta da zaune-tsaye, kamar yadda jaridun Najeriya suka ruwaito.
Rahoton kamar yadda shafin yanar gizon jaridar Daily Trust ya wallafa, ya bayyana cewa kungiyar ta ISWA na daukan mayakan matasa domin kai hare-hare, da nufin haddasa fitina a tsakanin kabilu da mabiya addinai daban-daban.
An gabatar wa da shugaba Buhari wannan rahoton ne bayan rikicin jihar Benue da sauran jihohi da suka kai ga salwantar da rayuka.
Wannan shi ne karon farko da hukumomin tsaron Najeriya, suka sanar a hukumance, cewa akwai ‘yan kungiyar ta ISWA a kasar, kamar yadda shafin yanar gizon jaridar Leadership ya wallafa.
Saurari hirar daya daga cikin jami'an yadan labarai a fadar shugaban kasar Najeriya, Malam Garba Shehu, a wannan rahoton da Umar Faruk Musa ya hada mana:
Facebook Forum