Taron da za a kwashe kwanaki hudu ana gudanarwa ya samu halartan manyan mutane daga Jihohi 36 har da Abuja ciki har da Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar da shugaban Kungiyar Kiristocin Nigeria ta CAN, Dr. Ayo Kunle da sauran wasu masu fada a ji a Najeriya.
Ustaz Muhammad Nurudin Lemo, yana cikin mahalartan taron kuma ya fadawa wakiliyar Muryar Amurka cewa kafin a cimma burin da aka sa a gaba, sai an kawar da rashin gaskiya tsakanin manyan malamai. Yace ya kamata mutanen da ake girmamawa ta bangaren addini su tabbatar da ganin an yi adalci a duk lokacin da irin wadannan matsaloli suka taso.
Da yake karin haske a cikin kasidarsa da ta mai da hankali a kan kauna, babban mai jawabi a wurin taron daga jami’ar Ahmadu Bello Zaria, Prof. James Kantiyok yace rashin wayewa da rashin fadin gaskiya su ne suke haddasa rikicin addini.
Wannan taron da aka shirya a kan zaman lafiya da kaunar juna bai bar mata a baya ba. Maryam Ibrahim Dada na cikin matan da suka halarcin taron kuma ta yi tsokaci a kan muhimmancin taron.
Ga dai Rahoton Madina Dauda:
Facebook Forum