Kudirin dai na kokarin kyautata gasa da neman baiwa kanana da matsakaitan ‘yan kasuwa da masu aikin kere-kere cikakkiyar damar gogayya da manyan kamfanoni da masana’antu ta fuskar kayayyakin da suke sarrafawa ko kuma ayyukan da suke gudanarwa a cikin kasa.
Alhaji Rabi’u M. Kura shine sakataren gamayyar kungiyoyin ‘yan kasuwa reshen jihar Kano kuma ya yi kira ga hukumar da alhakin ya rataya a wuyanta data taimaka wajan tabbatar da aiwatar da wannan kudiri nasu domin a cewar sa sun gaji a abin da ya kira kashin dankali, wato manta suna tattake kanana.
Hussaina Ahmad Umar, mataimakiyar masu kananan masana’antu ta kasa kuma mai zama da kuma masana’antar mangyada a jihar ta Kano ta ce sun halarci gangaminne domin nuna goyon bayansu a kan wanna kudiri.
Ta kara da cewa masu kananan masa’antu na samun tsaiko saboda manyan kamfanoni sun yi kaka gida, sun hana su sukunin gudanar da kasuwancin su da kuma samun ci gaba.
Matchin enable kungaiya ce dake karkashin hukumar kula da kasashe masu tasowa ta Burtaniya ta shirya wannan gangamin, da aka yi tattaki daga cibiyar ‘yan jarida ta jihar Kano zuwa harabar ma’aikatar yada labarum jihar.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari.