Jam’iyar dai na haramar karbar wasu manyan 'yan siyasar jihar ne ciki har da wasu yan takarar gwamna.Wanda hakan ke nuni ga sabuwar dambarwar siyasar jihar a tsakanin bangaren gwamnanan jihar da kuma wasu kusoshin jam’iyar APC dake Abuja.
A wajen wani taro a jihar, shugaban ma’aikatan gidan gwamnatin jihar Adamawa ke nan Abdulrahman Abba Jimeta,mai lakabin ko sama da kasa, zata hadu, ke bayyana adawarsu da batun komowar wasu kusoshin siyasar jihar zuwa jam’iyar su ta APC inda yace ba zata sabu ba su shirya gangamin karbar wani.
wannan ko na zama yar manuniya ce ga sabuwar dambarwar siyasar jihar a tsakanin bangaren gwamnanan jihar Sen.Muhammadu Bindo Umaru Jibrilla da kuma wasu kusoshin jam’iyar APC dake Abuja, wadanda ke tare da bangaren yan majalisar wakilai da na dattawa da su Babachur David Lawal, wato sakataren gwamnatin tarayya, wanda ake ganin suna dasawa da tsohon gwamnan jihar Murtala Nyako.
To sai dai kuma jam’iyar APC, a jihar tabakin shugaban riko na jam’iyar Alh.Ibrahim Bilal yace su suna maraba da kowa.
Baya dai ga wasu kusoshin jam’iyar PDP dake dasawa da shugaba Buhari,haka nan ma akwai tsohon dan takarar gwamna na jam’iyar SDP, da suka fafata da gwamna Bindo,wato Engr Markus Gundiri,kuma kamar yadda hadiminsa ta fuskacin harkokin yada labarai Mr Edward Wabundani,ya tabbatar
Shima ,a martaninsa game da zargin da ake masa sakataren gwamnatin tarayyar Mr Babachur David Lawal,yace ba da shi ba,wai gada a kotu!
Ga rahoton Ibrahim Abdul'aziz.