Lamarin ya auku ne a yammacin jiya litini, yayin da basaraken da mukarrabansa ke hanyarsu ta komawa gida daga wani kauye dake yankin na Bokkos, kamar yadda Mr Don Maren yayi wa wakiliyar Sashen Husa Zainab Babaji bayanin cewa,
"da misalin karfe uku na yamma muka sami labarin cewa an hallaka babban basaraken mu na Bokkos, da kuma wasu mutane guda uku wato da direban sa, da dan rakiyarsa da kuma matar dan rakiyar sa."
Mr Don ya kara da cewa wadanda suka tsira daga cikin tawagar marigayin sun yi zargin cewa fulani ne da suka fito suka tare su a hanya suka bude masu wuta, ya kuma kara da cewa akwai mutane uku dake kwance a asibiti ana yi masu magani.
Daga karshe ya bayyana cewa bai wuce wata guda ba da aka harbi maga takardar majalisar Bokkos gaba daya, sai kuma kwatsam ga wannan ya sake faruwa.
A bangaren Fulanin kuma, Hardon Bokkos Alhaji Yakubu Boro ya bayyana cewa da misalin karfe biyar zuwa shidda na yamma, kwamandan sojoji na sector 7 ya kira shi inda ya bayyana masa cewa a abinda yaje ya taras a Bokkos, to amma kwamandan bai bayyana masa irin jama'ar da suka aikata aika aikar ba kokuma wadanda suka kama.
Ya kuma kara da cewa dashi da jama'ar sa basa da matsala da abokan zaman nasu.
Ga rahoton Zainab Babaji daga jihar Filato.