Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Banka Wa Gine Ginen Gwamnati Wuta A Birnin Tripoli Bayan Da Zanga-Zangar Kin Gwamnati Ta Yi Tsanani

Gine-ginen da ke daura da mashigar ginin jami'an tsaron Libiya kenan ke cin wuta.
Gine-ginen da ke daura da mashigar ginin jami'an tsaron Libiya kenan ke cin wuta.

Shaidun gani da ido a babban birnin kasar Libiya, Tripoli, sun ce an banka wa gine-ginen gwamnati wuta a yayin da ‘yan gwagwarmayar adawa da jami’an tsaro da kuma magoya bayan gwamnati ke fafatawa a wani dada tsananin da zanga-zangar kin Shugaban Libiya Moammar Gadhafi ta yi.

Shaidun sun ce gine-ginen gwamnati da dama sun kama da wuta a yau Litini bayan da a karo na farko aka ji aman wutar bindiga da daren jiya Lahadi, a lokacin da masu zanga-zangar kin gwamnati su ka yi yinkurin kwace tsakiyar babban birnin kasar daga magoya bayan Gaddafi. Suka ce ‘yan sandan Libiya sun harba barkonon tsohuwa a kokarinsu na tarwatsa masu zanga-zangar.

Dan Gaddafi, Saif al-Islam, ya yi jawabi a gidan Talabijin din kasar cewa mahaifinsa na rike kam da ragamar iko kuma hukumar soji na mai biyayya a sa’ilinda yak e fuskantar zanga-zangar kin gwamnati mafi tsanani tun da ya karbi ragamar iko a juyin mulkin 1969. Saif al-Islam ya ce gwamnati za ta yaki al’amarin har zuwa ga mutum guda da ka rage, da mace guda da ka rake da kuma harsashi guda da ka rake don cigaba da zama bisa gadon mulki.

Kungiyar rajin kare ‘yancin dan adam da ke Amurka mai suna Human Rights Watch ya fadi jiya Lahadi cewa an kashe a kalla mutane 233 a zanga-zangar da aka yi ta kwana da kwanaki, akasari a birnin Benghazi na gabashin kasar, inda zanga-zangar farko ta samo asali. Likitoci a Benghazi sun ce an kashe akalla mutane 50 jiya Lahadi lokacin da jami’an tsaro su ka bude wuta kan wasu ‘yan zanga-zanga da masu halartar jana’iza.

XS
SM
MD
LG