Yan gudun hijira da yawan su ya haura dubu biyu mazauna karamar hukumar Gwoza dake jihar Borno wadanda ke zaune a sansanin Malkohe da Daware na kananan hukumomin Yola ta Arewa, da gire jihar Adamawa.
Sun koka da watsin da gwamnatin jihar Bornon tayi dasu.Na rashin aikewa da jamian ta da su kula da irin halin da suke ciki, ko kuma aike musu da kayayyakin agaji.
Binciken da muryar Amurka ta gudanar shine rabon da gwamnatin jihar Bornon su ziyarci su ziyarci sansanin yan gudun hijirar tunn watan maris lokacinnda aka kwato mata da yara sama da dari biyu daga sansanin sanbisa .
Shugaban yangudun hijira dake a wani muhalli na wucin gadi da aka samar musu a kauyen malkohe Mallam Idris Abdullahi, ya nuna takaicin sa na kasawar da wakilan su a majilisun dattawa dana wakilai suka yi na kai musu ziyara a sansanin su. Domin ganin irin halin da suke ciki.
‘’Shi kaman Sanata Ali Ndume ya sammu kwarai da gaske kuma bai jajanta muna koda dai-dai na rana daya, yace muna yan uwa yaya kuke ciki’’
‘’Mune muka zabe shi tun yana dan majilisar dokoki har yakai ga Sanataya sammu kwara da gaske ‘’
Ga dai Sanuuni Adamu da Karin bayani.