Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Fafutuka A Kano Sun Fara Batun Gawar Wani Matashi Da 'Yan Sanda Suka Kashe Shekaru 20 Da Su Ka Gabata


Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan Jihar Kano, Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Duk da cewa a jihar Kano ba a samu zanga zangar ENDSARS ko tarzomar fasa runbunan gwamnati ba, amma akwai tarin korafi kan zargin cin zalin da wasu ‘yan sanda suka yi wa fararen hula.

Irin wannan cin zalin kan haddasa samun raunuka har ma da rasa ruyuka a wasu lokuta, ba tare da hukunta wadanda ake zargi da aikata wadannan miyagun laifuka ba, kamar yadda ya kamata.

Babban labarin ban takaici shine na DPO Solomon Ngodo wanda ake yi wa lakabi da kwanta-kwanta, wanda yayi sanadin kashe wani matashi Auwalu a Unguwar Brigade fiye da shekaru 20 da suka wuce wanda har yanzu gawarsa ke kwance a Asibitin Murtala na birnin Kano.

Koda yake babban sufeton ‘yan sanda na wancan lokacin Marigayi Ibrahim Coomassie ya sallami DPO kwanta-kwanta daga aiki, amma ‘yan sanda sun gaza gurfanar da shi a gaban kotu.

Sai dai a ‘yan makonnin baya gamayyar kungiyoyin kare hakkin dan Adam ta farfado da wannan magana kuma Comrade Haruna Ayagi da ke zaman Daraktan kungiyar, shike bin Kadin lamarin. Ya ce, da farko sun san akwai gawar yaron amma ta ya zasu dauka, na biyu me ake ciki da batun shari’a domin daukar mataki na gaba.

Dangane da zargin ‘yan sanda da kashe wani matashi mai suna Saifullahi Sani dan Unguwar Kofar Mata a Kano a cikin watan jiya na Oktoba kuwa Comrade Ayagi, ya ce baicin jagorancin kai gawar asibiti, ‘yan sanda sun fada masa cewa wadanda suka aikata danyen aikin na nan a tsare kuma dangin marigayin sun aminta da bin kadin jinin dan uwansu.

Ko me ya sanya jiha irin Kano mai yawan al’uma ba ta shiga waccan zanga zanga ta ENDSARS ba? Kwamrad Abdulrazaq Alkali Daraktan kungiyar “Organization for Community civic Engagement” mai rajin shugabanci na gari, kuma mai mara baya ga harkokin gwagwarmaya, ya ce binciken da ya gudanar ya nuna cewa batun SARS bai damu al’ummar arewacin Najeriya ba, saboda galibi ma ba su san abin da ake kira SARS din ba.

Ya ce wadanda suka shiga zanga zangar ma ba saboda SARS kadai ne yasa suka shiga ba. Akwai dalilai da dama kamar kuncin rayuwa da tsadar rayuwa da sauransu, dan haka yakamata gwamnati talura da wadannan abubuwa.

Ga alama dai har yanzu da sauran rina a kaba ga wannan lamari na zanga zanga, da ya haddasa hasarar rayuka a wasu sassan Najeriya daya kawo rushe rundunar SARS.

A kalla dai za a iya cewa, yankin arewa maso yammacin Najeriya na farfadowa daga kalubalen ‘yan bindigar da kan sace shanu da mutane, amma akasarin mazauna yankin da ke zaman kananan ‘yan kasuwa da manoma na bukatar tallafi da samar da guraben aiki ga mata da matasa, musamman a bana da ambaliyar ruwa ta yi bana a galibin sassan yankin.

Ga Mahmud Ibrahim Kwari da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:31 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG