A wani abu da ake ganin ka iya zama babban cikas ga shugaba Donald Trump, ‘yan majalisar dokokin wakilai na bangaren Democrat a Amurka, sun fara binciken ko shugaban ya boyewa jami’an gwamnati da ke tabbatar da ka’idar aiki.
Binciken zai mai da hankali ne kan ko ya ba tsohon Lauyansa Michael Cohen wasu daruruwan dubban daloli, da nufin ya biya wata mai sana’ar fina-finan batsa da ake kira Stormy Daniels, domin ta rufe bakinta, kan zargin da take yi na cewa sun yi mu’amulla ta lalata da Trump, a wasu shekaru da suka gabata.
Wannan bincike da kwamitin na majalisar wakilai ya fara, bangare ne na wani babban bicike da sabbin wakilai a majalisar na bangaren Democrat ke yi, wanda ke ci gaba da samun karbuwa, watannin biyu bayan da suka karbe ikon majalisar.
Har ila yau, wasu kwamitoci uku na binciken wannan badakala da ta shafi shugaba Trump da wasu na hannun damansa.
Binciken na zuwa ne kwanaki biyu bayan da tsohon lauyan na Trump, Michael Cohen wanda aka kunyata, ya bayyana a gaban wani kwamitin majalisar, inda ya ba da bahasi kan zarge-zargen da ake yi wa Shugaba Trump dangane da yadda aka gudanar da yakin neman zabensa a shekarar 2016, da kuma shekarar farko da ya kwashe a kan kujerar shugabancin kasar ta Amurka.
Facebook Forum