Wannan sansanin yana dauke da mutane dubu 4, sai dai rayuwa cikin sa ba dadi ko kadan.
'Yan Ci Rani Daga Dajin Calais a Faransa Tare Da Wakilin Muryar Amurka, Babi na 2
Babban wakilin MDD Nicolas Pinault sailin da ya ziyarci sansanin dake wajen birnin arewacin Faransa. Suko wadannan sauran yan gudun hijira ne daga kasashen Afghanistan, Sudan,da Eritrea suke kokarin bi ta cikin bututun karkashin kasa domin tsallakawa zuwa kasar Ingila.

5
Wannan wani dan kasar Habasha ne ya tsaya gaban wakilin muryar Amurka, a sansanin dake birnin Clalais dake arewacin birni Faransa. (Nicolas Pinault/VOA).

6
Yan sanda biyu suke tattaunawa da wasu yan gudun hijira a kusa da Calais. (Nicolas Pinault/VOA).

7
Yan sanda ke sintiri a tashan jirgin ruwa dake birnin Calais domin inganta matakan tsaro. (Nicolas Pinault/VOA).

8
Injin din janareta ne na samar da hasken wutan lantarki a sansanin yan gudun hijira. (Nicolas Pinault/VOA).