Wannan sansanin yana dauke da mutane dubu 4, sai dai rayuwa cikin sa ba dadi ko kadan.
'Yan Ci Rani Daga Dajin Calais a Faransa Tare Da Wakilin Muryar Amurka, Babi na 2
Babban wakilin MDD Nicolas Pinault sailin da ya ziyarci sansanin dake wajen birnin arewacin Faransa. Suko wadannan sauran yan gudun hijira ne daga kasashen Afghanistan, Sudan,da Eritrea suke kokarin bi ta cikin bututun karkashin kasa domin tsallakawa zuwa kasar Ingila.

1
Wasu yan gudun hijira ne suke zagayawa cikin sansanin, wanda yake a wajen birnin Calais dake arewacin kasar Faransa. (Nicolas Pinault/VOA).

2
Wasu yan gudun hijira su biyu yan kasar Afghanistan suke wanke hannu su a sansanin yan gudun hijiran dake wajen birnin Calais dake arewacin birnin Faransa. (Nicolas Pinault/VOA).

3
Wasu yan kasar Sudan ne a cikin sansanin yan gudun hijira wannan yana a wajen birnin Calais dake arewacin birnin Faransa. (Nicolas Pinault/VOA).

4
Wani dan gudun hijira ne ke wasan kwallo a sansanin dake wajen birnin Calais dake arewacin birnin Faransa. (Nicolas Pinault/VOA).