Yawan man fetur din da ake sha a Najeriya a kullum ya yi matukar raguwa a kasa da shekara guda tun bayan darewar Shugaba Bola Tinubu kan karagar mulki a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Alkaluman da aka samu daga rahoton yawan motocin man da ake fitarwa a rana daga hukumar kula da cinikin albarkatun man fetur ta Najeriya (NMDPRA), ya nuna cewar zuwa ranar 20 ga watan Agustan da ya gabata ana shan litar fetur miliyan 4.5 a kowace rana.
Yawan fetur din da ake sha a kowace rana a watan Mayun 2023 ya kai lita miliyan 60, 000, a cewar NMDPRA.
kiyasin da aka yi ya rage yawan man da ake amfani da shi a kowace da kaso 92 cikin 100 bayan ranar 29 ga watan Mayun, 2023.
Fashin bakin rahoton da aka yi, ya nuna cewar daga cikin jihohin tarayyar Najeriya 36, 16 ne kadai suka samu kason man fetur daga babban kamfanin man Najeriya (NNPCL) a watan da ake nazari.
Hakan na nufin jihohin da basu samu kason man ba sun yi fama da karancinsa a watan Agustan da ya gabata.
Bayanan yadda nnpcl ya raba man tsakanin jihohi 16, sun nuna cewar jihar neja ta samu kaso mafi girma na tireloli 21, abinda ya kama lita 940, 000 a kowace rana, jihar Legas ce ta 2 da tirela 12 kwatankwacin lita 726, 001, sai Kaduna ita ma da tirela 12 mai lita 454, 001.
Sauran jihohin sun hada da Oyo wacce ta samu tirela 12 da lita 454, 001 sai Kano mai tirela 9 sai Ondo Mai tirela 6 da Kwara ita ma mai 5 da Edo mai tirela 4 da Abuja ita ma da tirela 4.
Jihohi irinsu Sokoto sun karbi tirela 4 daga NNPCL, sai Ogun wacce ta samu 3 sai ita ma Osun da 3, su kuwa jihohin Gombe da Benuwe da Eikiti da Kebbi tirela dai daya suka samu kowacensu.
A ranar 29 ga watan Mayun 2023 Shugaban Kasa Tinubu, yayi shelar kawo karshen biyan tallafi akan man fetur, wanda a wancan lokaci ya lakume kimanin Naira tiriliyan 12 cikin shekaru 10.
Tun daga wannan lokaci farashin man fetur yayi tashin gwauron zabo daga naira 195 akan lita guda zuwa kimanin Naira 1300 akan lita, abinda ya janyo hauhawar farashin kayayyaki kaiwa mizanin kaso 34.19 cikin 100 a watan Yuni da rabon da a ga irin haka shekaru 30 da suka gabata. Tuni dai ya ragu zuwa kaso 32.7 cikin 100 a watan Satumbar daya gabata.
Dandalin Mu Tattauna