Rahotanni daga Najeriya na cewa wasu ‘yan bindiga sun shiga Jam’iar Abuja da ke babban birnin tarayyar kasar sun sace mutum 6.
Lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Talata kamar yadda rahotanni suka nuna, kuma wadanda aka yi garkuwan da su ma’aikatan jami’ar ne da iyalansu.
Rundunar ‘yan sandan birnin na Abuja ta tabbatar da aukuwar lamarin kuma cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce ta baza jami’anta don bin sahun ‘yan bindigar.
Kazalika jami'an tsaron sun ce an kara tsaurara matakan tsaro a yankin jami'ar.
Gidan talabijin na Channels ya ruwaito cewa daga cikin wadanda aka yi garkuwar da su akwai farfesoshi biyu da wasu mutum hudu.
Bayanai sun yi nuni da cewa maharan sun kwashe sama da sa’a biyu suna ayyukansu a sashen gidajen manyan malaman jami’ar, ba tare da an samu dauki daga ko ina ba.
Matsalar garkuwa da mutane ta zama ruwan dare a biranen Najeriya musamman a arewaci inda ‘yan bindiga kan sace mutane don neman a biya su kudin fansa.
Jihohin Katsina, Sokoto, Kaduna, Neja da Zamfara sun kasance wadanda suka fi fuskantar wannan matsala amma a baya-bayan nan, birnin na Abuja da ke makwabtaka da Neja shi ma yana fama da kalubalen maharan.