‘Yan bindiga masu fashin daji da Gwamnatin Najeriya ta ayyana su a matsayin ‘yan ta,adda na ci gaba da afkawa garuruwa a yankuna daban- daban na jihar Nejan Najeriya.
Wannan al’amari dai yana matukar jefa dubban mazauna yankunan cikin wani yanayi na tashin hankali.
Malam Abdulkadir Muhamad Beri, mazaunin jihar, ya ce ko a ranar Lahadin nan da ta gabata sai da suka fafata da wadannan ‘yan fashin daji.
Musa Bawa, kwamandan ‘yan sa kai a yankin na Beri ya jaddada aukuwar wannan lamari.
A can yankin karamar Hukumar shiroro ma bayanai sun nuna cewa ‘yan fashin dajin sun yi aika-aikar da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da hukumomin jihar ba su tantance iyakarsu ba.
Gwamnatin Jihar Nejan ta tabbatar da kai harin, Amma sakataren Gwamnatin Jihar Alh Ahmed Ibrahim Matane ya ce yawan mutanen da aka ba da labarin an kashe bai kai haka ba.
Masu sharhi akan sha'anin tsaro suna ci gaba da bayyana bukatar kara matsa kaimi domin kakkabe wadannan ‘yan ta’adda.