Rundunar ‘yan sandan ta ce an kashe mutanen kauyen ne a lokacin da suke aikin girbin amfanin gona a kauyukan Nukundna da Wurukuchi a ranar Talata.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar Neja, DSP Wasiu Abiodun, a cikin wata sanarwa da ya fitar, ya ce “har yanzu ba a samu cikakken bayanin harin ba saboda yanayin dazuzzukan da kauyukan ke ciki”.
Abiodun ya ce jami’in ‘yan sanda na yankin ne ya jagoranci rundunar ‘yan sandan inda za su fara farautar ‘yan bindigar.
Ya kuma tabbatar wa al’ummar jihar cewa ‘yan sanda za su ci gaba da kare rayuka da dukiyoyin ‘yan kasa amma ya nemi a ba su bayanan da za su kai ga cafke ‘yan bindigan.
Wasu rahotani na cewa an kona wasu gidaje daya daga cikin kauyukan gabaki daya wanda hakan ya sanya wasu daga cikin mutanen kauyen suka nemi masauki da matsuguni a Kuta, hedikwatar karamar hukumar.