Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Akalla Dalibai 29 ne 'Yan Bindiga Suka Kashe a Hari da Suka Kai Kan Makarantar Tarayya a Buni Yadi Jihar Yobe


Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau
Shugaban kungiyar Boko Haram Abubakar Shekau

Hukumomin tsaro a jihar Yobe dake arewa maso gabashin Najeriya sun tabbatar da rahoton hari da 'yan bindiga suka kai kan wata makarantar gwamnatin tarayya dake Buni Yadi.

Wani mahaifi da dansa ya tsira daga harin da 'yan bindigan da ake kyautata zaton 'yan kungiyar ahlul sunna lid'da'awati wal-jihad ko Boko Haram ne suka kai, shi ya gayawa wakiliyar Sashen Hausa Sa'adatu Mohammed bayanai da suka samu kan yadda 'yan binidgar suka kai wannan mummunar hari.

Yace al'marin ya fara ne tun wajen misalin karfe 9 na dare lokacinda 'yan bindigar suka shiga makaranatar. Tun daga waje dan nasa da wasu suka ji an kamo wasu dalibai, maharan suka kuma kwaso wadansu daga dakunan kwanansu.

Mahaifin daya daga daga cikin daliaban dake makaranatar wanda bai bayyana sunansa ba, yace dan nasa da ya ji yamutsi da ihun takwarorinsa sai ya tsallaka ya fada cikin wani rami, yana jin kara da take taken abubuwa da 'yan bindigar suke yi.

Yace dan nasa suna kallon ana kama wasu daliban a jefa su cikin wuta, wasu kuma ana yankasu, babu harbin bindiga a harin baki daya. Malamin yace tun karfe tara na daren litinin, har zuwa karfe 3 na asuba babu dan kwana-kwana ko jami'in tsaro d a ya kaiwa daliban doki duk da cewa akawai jami'an tsaro a Buni Yadin.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG