‘Yan bindigan Boko Haram a Najeriya sun kashe mutane 98 a garin Bama dake arewa maso gabashin kasar, a makon da ya wuce kamar yadda mazauna garin suka shaida. ‘Yan bindigan sun kaiwa garin farmaki ne a safiyar Laraba, 19 ga watannan na Fabrairu, inda suka bude wuta akan wata makaranta, suka harbe mutane da yawa, kuma suka kona mutane, tare da kona fadar daya daga cikin masarautun Musulunci da suka fi tsufa a yammacin Afirka.
Barnar da Harin Boko Haram Yayi a Bama, Fabrairu 20, 2014
![Wasu mazauna garin Bama da suka raunata sakamakon harin Boko Haram, suna jiran ganin likita a Asibiti, Fabrairu 20, 2014.](https://gdb.voanews.com/68371234-c746-48c1-ac5c-a214afe016ba_cx3_cy7_cw96_w1024_q10_r1_s.jpg)
1
Wasu mazauna garin Bama da suka raunata sakamakon harin Boko Haram, suna jiran ganin likita a Asibiti, Fabrairu 20, 2014.
![Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram a Bama, Fabrairu 20, 2014.](https://gdb.voanews.com/6a3ecc20-0fdc-4633-898b-af63a5df5ac5_cx0_cy4_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
2
Gidajen da suka kone bayan hare-haren Boko Haram a Bama, Fabrairu 20, 2014.
![Wasu mazauna garin Bama da suka raunata sakamakon harin Boko Haram, suna jiran ganin likita a Asibiti, Fabrairu 20, 2014.](https://gdb.voanews.com/1e4c83c9-917f-4318-91db-adb46676bf07_cx7_cy14_cw92_w1024_q10_r1_s.jpg)
3
Wasu mazauna garin Bama da suka raunata sakamakon harin Boko Haram, suna jiran ganin likita a Asibiti, Fabrairu 20, 2014.
![Wata mota dauke da kayan jama’a, akan hanyarta na fita daga Bama, Fabrairu 20, 2014.](https://gdb.voanews.com/da17b20a-7502-4ed3-9eda-21dd4fbf5b9a_cx0_cy9_cw0_w1024_q10_r1_s.jpg)
4
Wata mota dauke da kayan jama’a, akan hanyarta na fita daga Bama, Fabrairu 20, 2014.