Wasu ma'aikatan jirgin saman da kuma jami'an filin jirgin biyu sun ce wasu mutane dauke da makamai sun shiga harabar filin jirgin ta wani shinge daga wani dajin da ke kusa kuma suka fara harbe-harbe ba da jimawa ba don tsoratar da ma'aikatan.
"Sun bude wuta ma jami'in tsaron Hukumar Kula da Sararin Samaniya ta Najeriya (NAMA) ko kuma (Nigerian Air Space Management Agency), inda nan take su ka kashe shi kuma suka yi kokarin kutsawa cikin titin jirgin don hana (wani) jirgi tashi," in ji ma'aikatan jirgin da suka ki a bayyana sunansu saboda ba su da ikon yin magana da manema labarai.
Jami’an filin jirgin biyu sun ce jami’an tsaro dauke da makamai sun yi nasarar dakile ‘yan bindigar, tare da hana su shiga babban harabar filin jirgin.
Mai magana da yawun rundunar ‘yan sandan jihar Kaduna bai amsa kiran da aka yi masa ba, ko kuma sakon tes na wayar hannu na neman karin bayani.
‘Yan bindiga dai na cigaba da tabka ta’addanci a yankin arewa maso yammacin Najeriya, inda suke kai hare-hare tare da kashe mutanen gari da jami’an tsaro da kuma yin garkuwa da daruruwan yara ‘yan makaranta da mazauna kauyuka domin neman kudin fansa.
~ REUTERS