Shaidu sun ce karshenta ginin kamfanin, wanda ke tsakiyar birnin Tripoli, ya kama da wuta bayan kai farmakin, wanda shine irinsa na farko da aka taba kaiwa kan kamfanin na N.O.C.
An dai shawo kan lamarin koda yake ma’aikatan tsaro sun cigaba da farautar maharan a cikin ginin, a cewar wani kakakin jami’an tsaron kasar, Ahmed Ben Salem.
Rahotanni sun ce an kashe biyu daga cikin ‘yan bindigar, amma har zuwa yanzu ba wata kungiya da ta dauki alhakin kai harin.
Wannan al’amarin dai ya faru ne kwana daya kacal bayanda aka fara aiwatarda wani shiri na tsagaita wuta wanda majalisar dinkin duniya ta shirya bayanda aka kashe mutane 61 a kazamin fadan da ya kaure kwanan baya tsakanin kungiyoyin ‘yan banga na Libya.
Facebook Forum