Matakin da gwamnan jihar Agadez ya dauka a baya bayan nan don hanawa wasu ‘yan fafutika gudanar da mahawara, shine ya farfado da kace-nace a tsakanin gwamnatin Nijar da alkalan Shari’a, wadanda suka fitar da sanarwa domin jan hankalin shugaban kasa Issouhou Mahamadou.
Mai shara’a Zakari Yaou Mahamadou, shine sakataren tsare tsaren kungiyar SAMAN. Ya ce sun ga wannan abu ya faru shekaru biyu da suka gabata, inda wani alkali a Damagaram ya saki wasu mutane, amma gwamnan jihar na wancan lokacin yasa aka sake kamasu tare da tsaresu. Haka kuma irin wannan abu ya faru a garin Maradi.
Da yake maida martani wa kungiyar ta alkalai ministan Shari’a Marou Amadou, ya ce labarin ba haka yake ba.
Jarabawar cancantar shiga aikin shari’a da aka gudanar a watannin da suka gabata, wani abu ne da kungiyar SAMAN ta ce yana bukatar a gudanar da bincike akan sa don tantance zahirin abubuwan da suka wakana.
Rashin kayan aiki a kotuna wani abu ne da bangarori ke ja in ja akan sa yayin da kungiyar alkalai ke cewa karancin kayan aiki na haddasa cikas, a sha’anin aiki labarin ya sha bamban a wajen gwamnati.
Takun saka tsakanin gwanatin Nijar da kungiyar alkalai ta SAMAN ba bakon abu ba ne, kamar yadda a wani lokacin baya kungiyar ta bukaci shugaban kasa ya damka ministan kudi Hassoumi Massaoudou a hannun Shari’a, domin ya yi bayani akan zargin alkalai da nuna bangaranci akan aiki sai dai wannan haka ba ta cimma ruwa ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma.
Facebook Forum