Kasar Afrika ta kudu ta shiga mako na bakwai a rufe yayin da ta takaita al’ammurra domin dakile yaduwar cutar coronavirus.
Manyan jami’an kasar na ganin ta hakan an sami nasara sosai wajen hana yaduwar cutar, amma masu suka na ganin ya kamata a bude kasar, sakamakon tsananin talauci, rashin raba-daidai da kuma rashin aikin yi da aka dade ana fuskanta a kasar.
Al’umma sun nuna matukar gajiya da zaman kulle da aka kakaba musu. Mahukunta ma sun yarda cewa kullen ya taba tattalin arzikin a’lumma da lafiyar kwalkwalwasu, amma sun ce sun yi hakan ne saboda kare lafiyarsu, inda kasar ta rasa kaso 3.2 na adadin wadanda hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta ayyana sun mutu sanadiyar cutar a Afrika.
Kididdigar da WHO ta fitar, ta nuna cewa kusan kashi 7 cikin dari na wadanda suka kamu da cutar ne suka mutu a fadin duniya baki daya.
Shugaban jam’iyar Democratic Alliance dake adawa a kasar, John Steenhuisen, ya jefawa jam’iyya mai ci ta ANC kalamai masu zafi cewa, “mun daina yaki da cutar COVID-19. Mu na fama ne da kulle mu da akayi. A takaice kullewar ANC… Bari in fada karara, babu dalilin ci gaba da kulle mu”
Facebook Forum