Ma’aikatar Lafiya a Sudan Ta Kudu ta yi gargadin cewa ana iya fuskantar mummunar barkewar cutar coronavirus a kasar, ganin yadda masu dauke da ita ke kin ba da hadin kai ga jami’an kiwon lafiya.
Dakta Thoi Loi, mai magana da yawun Ma’aikatar Lafiya Ta Sudan Ta Kudu, ya fadawa manema labarai a birnin Juba cewa, wajibi ne mutane su rika bayar da tazara sannan su rika bayar da hadin kai ga jami’ai don a dakile yaduwar cutar, ko kuma wani abu da ka iya ma fin hakan muni.
“A kauce ma duk harkokin da ke kawo haduwar jama’a, a ci gaba da yawaita wanke hannuwa, a kuma kauce ma shan hannu; muddin muka ki yin haka, to za mu fuskanci mummunar barkewar COVID-19 a kasar,” a cewar Dakta Loi a wani shirin gidan rediyon Muryar Amurka game da batutuwan Sudan Ta Kudu, mai suna South Sudan in Focus a turance.
Facebook Forum