A Jamhuriyar Nijer ‘yan bindiga sun kai hari a wasu kauyukan yankin Tilabery mai makwabtaka da kasashen Mali da Burkina Faso a karshen mako, inda suka yi nasarar hallaka mutane akalla 20, yayin da a dai-dai wannan lokaci jami’an tsaro suka yi nasarar murkushe wani harin da mayakan Boko Haram suka kai wa gadar garin Dutsi dake iyaka da Najeriya.
Rahotanni daga yankin Tilabery sun bayyana cewa da misalin karfe 4 na yammacin Asabar ne ‘yan bindiga a kan babura suka afkawa wadannan kauyuka cikin wani yanayi na ba zata.
A kauyen Gadabo, maharan sun kashe mutane 7 su ka ji wa wasu 3 munanan raunuka, haka kuma sun hallaka mutane 3 a kauyen Zibane koirategui, kafin su bindige wasu mutanen 10 tare da jikkata wasu 2 a kauyen dake karkarar Anzourou.
Gwamnan Tilabery Tijani Ibrahim Katchiella wanda ya halarci jana’izar mamatan, ya jajantawa al’umomin kauyukan, sannan ya tabbatar masu da cewa gwamnati za ta dauki dukkan matakai don kare jama’a da dukiyoyinsu.
Tagwayen hare-haren na karkarar Anzourou sun sake farfado da mahawara a dangane da yanayin tsaro a yankin Tilabery. Jami’in fafutuka Ibrahim Mamoudou ya ce akwai bukatar gwamnati ta sake duba tsarin tattara bayanan sirrin dake shigowa ga jami’an tsaro daga jama’a.
A yankin Diffa mai fama da rikicin Boko Haram, an fuskanci farmakin ‘yan ta’adda a gab da gadar garin Dutsi dake iyakar Nijer da Najeriya a shekaran jiya Asabar, amma jami’an tsaron na Nijer sun fatattake su zuwa inda suka fito, kuma wannan shi ne karo na uku da Boko Haram ke yunkurin kai hari a gadar ta Dutsi a cikin kasa da mako biyu.
Saurari Karin bayani cikin sauti daga Souley Moumouni Barma.
Facebook Forum