Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan adawa Sun Yi Tir Da Matakin Sabuwar Majalisar Dokokin Venezuela


Majalisar Dokokin Venezuela mai samun goyon bayan 'yan adawa
Majalisar Dokokin Venezuela mai samun goyon bayan 'yan adawa

Majalisar dokokin kasar Venezuela da ‘yan adawa ke jagoranta, ta yi wani zama a jiya Asabar, inda ta yi watsi da karfin ikon da sabuwar majalisar dokokin kasar ta baiwa kanta na yin doka.

Majalisar dokokin 'yan adawa a kasar Venezuela ta yi Allah wadai da matakin da sabuwar majalisar dokoki mai samun goyon bayan gwamnati ta dauka na bai wa kanta ikon yin doka.

Kakakin ‘yan adawa Freddy Guevara, da ba a ka da shi a magana, da kuma mataimakin shugaban majalisar, sun yi Allah wadai da ikon da sabuwar majalisar ta baiwa kanta, inda suka ce matakin “haramtacce ne.”

Majalisar dokokin dake samun goyon bayan ‘yan adawar kasar, sun fitar da wannan matsaya ta su ce a gaban jami’an diplomasiyyar kasashen Amurka da Burtaniya da Mexico da kuma Spain ko kuma Andalus.

Wannan zama da majalisar dake samun goyon bayan ‘yan adawa ta yi, martani ne ga matsayar da sabuwar majalisar dokokin kasar ta dauka na bai wa kanta karfin ikon yin doka da karbe ikon ainihin majalisar dokokin kasar da ke hannun ‘yan adawa.

Ko da ya ke matakin sabuwar majalisar bai rushe majalisar ‘yan adawan ba, amma kuma ya mai da ita tamkar ta jeka-na-yi-ka.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG