Da yake mika tallafin ga ministan harkokin wajen Turkiyya a madadin gwamnatin Najeriya, jagoran tawagar Ministan babban birnin tarayyar Najeriya Abuja, Mallam Muhammad Musa Bello, ya ce shugaba Buhari da kansa ya yi niyyar zuwa Turkiyya, Amma saboda yanayi na zabe da ake ciki a Najeriya bai samu dama ba.
Daga nan ministan ya mikawa gwamnatin Turkiyyar gudunmawar dalar Amurka miliyan daya da wasikar ta'aziyya da jaje bisa girgizar kasar, inda ya yi fatan Allah ya jikan wadanda suka rasu, kana ya bawa wadanda suka sami raunuka lafiya, ya kuma kiyaye aukuwar hakan nan gaba.
Da yake amsar tallafin a madadin gwamnati da al'ummar Turkiyya, ministan harkokin wajen Turkiyya, Jakada Casavuglu, ya bayyanawa tawagar Najeriya cewa shugaba Recep Tayyib Erdoghan ne da kasansa ya so ya tarbi tawagar Najeriyar, amma saboda yana can yankin da abin ya faru kuma dakansa yake jagorantar ayyukan ceto dalili Kenan da yasa hakan bai faru ba.
Ambasada Casavuglu, ya ce tunda farko itama uwargidan shugaban Najeriya, Aisha Buhari, ta aike masu da tallafin barguna 10,000 don rarrabawa ga wadanda ibtila'in ya shafa, ya na bayanin cewa kawo yanzu kimanin mutane dubu 24,000 ne suka rasa rayukansu kana wasu milyan goma sha daya kuma sun daidaice.
Yana bayyana cewa kimanin yankuna goma sha daya a kudancin kasar abin ya shafa da suka hada da Adana da Adiyaman da Diyarbakir da Gaziantep da Hatay da Kahramanmaras da Kilis da Malatya da Osmaniye da Sanliurfa, da kuma Elazig.
Domin karin bayani ga rahotan Hassan Maina Kaina.