Akwai alamar sake gani tashin hankali da rigingimu, a cikin yanayi na yawan rikici a DR Congo, yayin da kasar ke shirin yin zaben da aka dade ana dagewa a ranar 23 ga watan Disemba.
‘Yan adawa da kawunansu ke rarrabe, sun kyautata zaton zasu yi galaba a kan jami’iya mai mulki karkashin dan takararta Emmanuel Ramazani Shadary dake samun goyon bayan dadadden shugaban kasar Joseph Kabila. Kabila yana shirin ajiye shugabancin kasar, bayan yaki yarda ya sauka daga karagar mulki a lokacin wa’adinsa ya kare a cikin watan Disemban shekarar 2016.
Bayan wata tattaunawar wuni biyu a babban birnin Afrika ta Kudu Pretoria, wasu shugabannin ‘yan adawa su bakwai sun amince a kan wasu muhimamman batutuwa guda biyu, a cewar wasu takardu da daya a cikin shugabannin ya aikewa Muyar Amurka a jiya Juma’a.
‘Yan adawan sun amince zasu shiga zaben, duk da cewa suna da damuwa game da yanayin siysasar kasar da kuma rashin yardarsu da tsarin kada kuri’a na zamani da suke ganin yana tattare da aibi ko kuma ba za a gane amfani da shi ba.
Sun kuma amince zasu fitar da dan takara daya. Sai dai wata dadaddiyar mai fashin baki a Congo Stephanie Wolters tace wannan batu na da rikitarwa.
Facebook Forum