Al’ummar Tunut ta dauki wannan matakin ne na jan hankalin hukumomi bayan sun shafe shekaru bakwai suna fama da matsalar wutar lantarki. Rahotanni na nuni da cewa, tunda aka fara samun matsalar kamfanin samar da wutar lantarki ya shiga kokarin neman hanyar shawo kan matsalar sai dai ba a dace ba
A cikin hirarshi da Muryar Amurka, daraktan kamfanin gidan wuta na jihar Damagaram, Suleiman Mummuni yace daukar wannan matakizai kawo karshen matsalar a garin na Tanut, sabili da za su kara janyo wata wutar daga cibiyar su da take SORAZ don wadata sauran garuruwan dake kewaye da Tanut.
Hukumomi sun bayyana cewa, za a fara aikin jan wutar lantarkin ne a shekara ta dubu biyu mai kamawa, abinda al’ummar yankin suka ce zasu sa ido daga nan zuwa shekara guda suga ci gaban da aka samu na zahiri.
Saurari Cikakken rahoton Tamar Abari
Facebook Forum