Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yakamata Duniya ta Sake Yadda Take Kallon Nahiyar Afirka-Barack Obama


Shugaban Amurka Barack Obama
Shugaban Amurka Barack Obama

Shugaba Barack Obama ya zama shugaban Amurka na farko dake kan karagar mulki da ya yiwa taron kungiyar kasashen Afirka jawabi

Shugaba Obama yace lokaci ya yi har ma ya shige na cigaba da daukar nahiyar Afirka a zaman inda talauci da rikice-rikice suka samu gidin zama na har abada.

Tilas duniya tayi na'am da irin gagarumin cigaba da nahiyar tay a fannoni da dama cikinsu har da fannin kiwon lafiya. Yawan yaran da suke mutuwa a sanadin malariya ya ragu. A yanzu Afirka ita ce ke jagorancin duk duniya wajen tura karin yara zuwa makarantu.

A yayinda Afirka take canzawa haka kuma na bukaci duniya ita ma ta sauya yadda take tunkarar Afirka. 'Yan Afirka da dama sun sha fada mini cewar su fa ba wai bara suke yi ba. Cinikayya suke son kullawa wadda zata taimaka ga cigabansu. Su ba iyayen gida suke nema ba. Abokan hulda suke nema wadanda zasu taimaka masu wajen gina kasa ba wai zubda mutuncinsu wajen dogaro akan wasu ba. So suke yi su zabi abun da ya dace musu da kuma makomarsu.

Bayan haka kuma a zaman Afirka a nahiyar da tafi bunkasa yawan al'ummarta zai nunuku cikin wasu 'yan shekaru zuwa mutane miliyan dubu biyu kuma akasarinsu zasu kasance matasa 'yan kasa da shekara goma sha takwas. Wannan na iya zamowa wata kyakyawar dama to amma kuma idan ka kalli abubuwan da suke faruwa a yankin gabas ta tsakiya da kuma Afirka ta arewa zaka gane cewa barin matasa masu dimbin yawa babu aikin yi kuma babu hanyar bayyana kokensu na iya haddasa fitina da rashin bin doka da oda a kasa. A saboda haka shawarata a gareku itace babban kalubalen dake gaban Afirka a yanzu da kuma shekarun dake tafe shi ne samarda dama ga wadannan matasan. Aiki ne babba domin dole ne Afirka ta samarrda miliyoyin ayyukan yi sabbi kuma lokaci na neman kurewa. Irin zabin da zaku yi a yanzu zai tantance makomar nahiyar Afirka a cikin shekaru masu yawa da suke tafe.

Ina wa'adina na biyu akan mulki. A karkashin tsarin mulkinmu ba zan iya sake tsayawa takara ba. Ina kwadayin aikina kuma na san ina yinsa yadda yakamata to amma doka doka ce. Babu wanda ya fi karfin doka koda shugaban kasa. Idan har shugaban kasa ya nemi canje dokokin kasa yayinda yake kan mulki domin ya cigaba da yin mulkin to ya jefa kasa cikin fitina kamar yadda muka gani a Burundi. Idan har shugaban kasa na jin cewar shi kadai ne zai iya mulkin kasa to lallai bai tabukama kasar tasa komi ba ke nan. Kamar yadda kungiyar tarayyar Afirka ke yin tur da juyin mulki zata iya kuma taimakawa al'ummar Afirka ta hanyar tabbatar da cewa shugabanni suna mutunta wa'adin da yakamata su yi akan mulki. Babu wanda ya cancanci zamowa shugaban kasa na har illamasha allahu.

A yankin tafkin Chadi sojojin kasashe da dama tare da goyon bayan kungiyar tarayyar Afirka suna kokarin kawo karshen zub da jinin rashin kan gado da rashin imani na kungiyar Boko Haram. Muna jinjinawa duka wadanda suke sadakar da kawunansu domin kare fararen hula da jama'ar da basu ji ba basu gani ba cikinsu har da sojojin kiyaye zaman lafiya masu yawa. Yayinda Afirka take yakar ta'adancin Amurka tana nan daram a bayanta. Muna kara karfin sojojin Afirka ta hanyar horaswa da bada tallafi. Tilas sauran duniya su tallafawa wannan yunkurin.

Kadan ke nan daga cikin abubuwan da shugaban Amurka ya tabo a jawabinsa ga taron koli na kungiyar tarayyar kasashen Afirka.

Ga bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:27 0:00

XS
SM
MD
LG