Shugaban Amurka Barack Obama yace Amurka da Kenya sun hada kai a yaki da ta'addanci.
Da yake magana yau Asabar a taro da manema labarai na hadin guiwa da shugaban kenya Uhuru kenyatta, shugaba Obama yace Amurka da Kenya suna aiki tare sosai dangane da matakan yaki da ta'addanci musamman yadda suke tunkarar al-shabab.
Haka nan shugaba Obama ya godewa kenya saboda samar da muhalli ga 'yan gudun hijira daga Somalia wadanda fadace fadacen ta raba da muhallansu.
Shugaba Obama yace kenya tana da 'yan jarida wadanda suka san aikinsu mataki d a yace yana taimakawa kasa ta zama main karfi. Mr. Obama yace Amurka tana aiki da Kenya domin tunkarar barazana ga ci gaban kenyan. Ya kuma yabawa shugaba kenyatta bisa kudurinsa na yaki da cin hanci da rashawa, da kuma kara ganin ana gudanar da aikin gwamnati ba tareda kunbiy-kunibiya ba.
Anasa bangaren shugaba kenyatta yace Amurka da Kenya, suna da muradu da al'adu iri daya a fannoni daban daban. Yace Kenya tana kara zurfafa salon mulkin demokuradiyya, yayinda kuma take yaki da ta'addanci.