Daga nan kuma zai sauka a Adis Ababa a matsayin shugaban Amurka na farko da ya ziyarci kasar Ethopia. Ya kamala ziyarar ne da halartar liyafar da shugaban kasar Kenya Uhuru Kenyatta ya shiya masa.
Obama yayi nuni da cewa mahaifinsa da mahaifin Uhuru na Kenya sun san juna, yace bai san farin cikin da zasu yi ba inda zasu san ga ‘ya’yansu a waje daya.
Mista Obama ya jaddada cewa Amurka da Kenya zasu hada karfi da karfe wajen yakar ta’addancin ‘yan kungiyar Al-Shabaab na Somalia.