Cibiyar nazarin aikin lafiya ta Amurka-NIH- ta fitar da wani samakon bincike da zai shafi rayuwar miliyoyin kananan yara, da matasa, da yaran dake cikin kuruciya wadanda ko dai suke dauke da kwayar cutar HIV ko kuma suke fama da cutar kanjamau.
Binciken na nuni da cewa, shan maganin dake dauke da sinadarin gina jiki na bitamin D zai taimaka wajen rage karfin kashin da maganin kashe kaifin cutar kanjamau da ake kira tenofovir. Cibiyar nazarin aikin lafiya na Amurka ta fitar da wannan rahoton ne ranar goma ga wannan watan na Janairu.
A cikin wani binciken kuma, masu bincike na cibiyar da kuma abokan aikinsu sun gano wani sabon hadarin da jariran dake dauke da cutar kanjamau tun suna cikin uwarsu suke fuskanta. Bisa ga binciken, suna iya fuskantar matsalar nauyin baki, watau dadewa basu yi Magana ba, ko kuma kasa fahimtar Magana ko bayyana kansu.
Bisa ga binciken cibiyar NIH, Adadin kananan yaran dake fama da nauyin baki tsakanin wadanda ke dauke da kwayar cutar HIV kafin haihuwarsu ya ruba na wadanda basu dauke da kwayar cutar. Sabili da haka, cibiyar ta bada shawara cewa, a yi cikakken bincike kan yaran da iyayensu ke dauke da cutar kwayar kanjamau domin tabbatar da cewa basu fama da nauyin baki.
Binciken ya yi nuni da cewa, jinya tana taimakawa wadanda suke dauke da kwayar cutar gaya. Yaran da basu samun jinya suna cikin hadarin har rubi uku na fama da nauyin baki fiye da matasan da ke dauke da kwayar cutar HIV da suke shan magani.
Cibiyar NIH wadda take da makarantu da kananan cibiyoyin bincike 27, ta kasance cibiya mafi girma dake daukar nauyin bincike a duniya. Ranar kanjamau ta duniya, Shugaban Amurka Barack Obama ya jadada kudurin Amurka na ci gaba da daukar nauyin bincike domin shawo kan cutar da kuma matsalolin da take haddasawa a duniya.
A shekara ta dubu biyu da goma sha daya, Amurka ta yi jinyar sama da mutane miliyan hudu dake dauke da kwayar cutar HIV yayinda ta kuma tallafawa sama da mutane miliyan goma sha uku da cutar kanjamau ta shafa da suka hada da sama da marayu da marasa galihu miliyan hudu da dubu dari.