Masu masaukin baki Kamaru sun fara zubin kwallayensu a teburin gasar cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON da ake yi a kasar.
Kamaru ta doke Burkinsa Faso da ci 2-1 a wasan bude gasar da aka yi a ranar Lahadi.
Burkina Faso ce ta fara zura kwallo a ragar Kamaru, daga baya masu masaukin bakin suka yunkuro suka musu lilis da kwallaye biyu.
Ita kuwa Ethiopia ta gane kurenta ne a hannun Cape Verde da ci daya mai ban haushi.
A ranar Litinin Senegal za ta hadu da Zimbabwe, Guinea da Malawi, Morocco da Ghana sai Comoros da Gabon.
Wani dan wasa da za a sakawa ido shi ne zakaran Liverpool Sadio Mane wanda zai fuskanci ‘yan kasar Zimbabwe.
Wani wasa kuma da ake ganin zai ja hankali shi ne wasan Najeriya da Masar (Egypt) wanda za a yi ranar Talata.