Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yadda Ra'ayin ‘Yan Majalisar Dattawa Ya Banbanta Kan Kasafin Kudin 2022


Shugaba Buhari ((Facebook/Femi Adesina))
Shugaba Buhari ((Facebook/Femi Adesina))

Ciyo bashin naira triliyon sama da 6 da za a yi kasafin kudin don rufe gibi, shi ne batun da ya fi daukan hankalin Shugaban Majalisar Dattawa Sanata Ahmed Lawal.

Gibin Naira triliyan 6.26 da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya ce sai an ciwo bashi kafin a toshe shi a kasafin kudi mafi girma da kasar ta taba samu, ya dauki hankalin shugaban Majalisar Dattawa Ahmed Lawan da wasu ya'yan majalisar,

Hakan ya sa mambobin majalisar suka bayyana ra'ayoyi mabanbanta akan matakan da majalisar za ta dauka don ganin kasafin ya yi wa al'umman kasa tasiri.

Wannan kasafi da Shugaba Buhari ya yi wa take da kasafi na samar da ci gaban al'umma, ya samu ra'ayoyi daban-daban daga mambobin majalisar dokokin kasar, ciki har da Shugaban majalisar Dattawa Ahmed Lawan wanda ya nuna damuwarsa akan yadda aka samun wagegen gibi a kasafin.

Lokacin da shugaba Buhari ya ajiye kasafin kudin 2022 a gaban majalisa (Facebook/Femi Adesina)
Lokacin da shugaba Buhari ya ajiye kasafin kudin 2022 a gaban majalisa (Facebook/Femi Adesina)

A cewar Sanat Lawal, dole ne majalisar ta yi aikin tantance kasafin daki daki domin a rage yawan wasu kudade da za su samu shiga lalitar gwamnati wajen toshe gibin.

Shi kuwa Sanata Abdullahi Adamu daga Jihar Nasarawa, ya yarda ana ciwo bashi amma yana ganin ba Najeriya kadai ke cin bashi ba.

Abdullahi ya ba da misali da kasar Birtaniya da ya ce yanzu haka ana bin ta bashin fam triliyan 3, wanda a ganin sa ya ma fi bashin da ake bin Najeriya.

Ya kara da cewa abin da za a duba shi ne a tabbata ana aiki da kudaden domin kyautata rayuwar ‘yan Najeriya.

A lokacin da yake nashi nazarin, Sanata Barau Jibrin wanda yake shugabantan Kwamitin Kula da Kasafin kudi a Majalisar Dattawa, ya yaba ne da irin ayyukan more rayuwa da za a yi da kasafin inda ya ce za a zaburad da tattalin arzikin kasar ne saboda masu kananan sana'o'i su samu ayyukan yi .

Amma Sanata Abdullahi Ibrahim Danbaba ya ce ba anan gizo ke saka ba.Inda ya ce girin-girin ba, ta yi mai shi ne alfanun kasafin kudi.

Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))
Lokacin da Buhari yake gabatar da kasafin kudin 2022 a gaban majalisar dokoki ((Facebook/Femi Adesina))

Ya kara da cewa duk shekara za a yi kasafin kudi amma babu abin da ke sauyawa.

Ibrahim ya ce ya yi bincike akan kasafin da ake yi a kasa tun shekara 2016 amma kullum sai an cusa wasu ayyuka na daban da wanda shugaban kasa ya yi a kowane kasafi.

A wannan Kasasfi na shekara 2022, za a yi amfani da Kashi 22% cikin dari ne wajen sayo kayan tsaro, Naira triliyan 3.61 wajen biyan basussukan da aka ci a baya, sannan a yi amfani da Naira triliyan 4.11 wajen biyan albashin ma'aikata, su kuma ‘yan fansho an ware masu Naira biliyan 579.

Duka duka dai za a kashe Naira triliyan 16.39 a matsayin kasafin kudin shekara 2022.

Saurari cikakken rahoton Medina Dauda daga Abuja:

Yadda Ra'ayin ‘Yan Majalisar Dattawa Ya Banbanta Kan Kasafin Kudin 2022 - 3'12"
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:12 0:00


XS
SM
MD
LG