Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mabanbantan Ra'ayoyi Kan Yarjejeniyar COP28 Da Kasashen Duniya Suka Cimma


Taron Yanayi COP28
Taron Yanayi COP28

Shugabannin duniya da wakilai daga kasashe kusan 200 da suka halarci taron sauyin yanayi na COP28 a Dubai, sun cimma wata muhimmiyar yarjejeniya ta sauya sheka daga amfani da albarkatun mai.

Yarjejeniyar dai ba ta samu karbuwa a Najeriya ba, wacce ta dogara da sayar da danyan mai a mafi yawan kasafin kudinta, inda shugabannin suka ce suna bukata kudade, idan har duniya na son kasar ta sauya sheka daga amfani da kuma hako albarkatun mai.

A ranar Laraba ne aka rufe babban taro kan yanayi na COP28 a Dubai, inda aka rattaba hannun kan yarjejeniyar sauya sheka daga man fetur da iskar gas da kuma kwal a cikin abin da daftarin ya bayyana da daidaicewa da ingantaccen tsari, da ke fatan rage gurbatacciyar iska da saukaka dumammar yanayi.

Wannan dai ita ce irin wannan yarjejeniya ta farko da za ta kaucewa amfani da albarkatun mai, tun bayan da aka fara taron na shekara-shekara, kusam shekaru talatin da suka wuce.

Yarjejeniyar ta kuma nemi rubanya yawan sabon makamashi mai tsafta a duniya nan da shekarar 2030, tare da inganta fasahar zuke gurbatacciyar iskar carbon da za su iya tsaftace masana’antu masu wuyar tsarkakewa.

Shugaban COP28, Sultan Al Jaber na Dubai, ya yaba da yarjejeniyar, amma ya ce aiwatar da ita ne zai nuna nasara ta gaskiya.

Peter Tarfa, tsohon daraktan kula da yanayi a ma’aikatar muhalli ta tarayyar Najeriya, ya amince da hakan.

Ya ce “Ba wannan ne karon farko da aka cimma matsaya kan tattaunawar sauyin yanayi a taron bangarorin da ba’a aiwatar da su gaba da yaba. A zahiri ya na da kyau ga yanayi da kowa ya kamata ya sa hannu a ciki.”

Sai dai wasu ba su ji dadin yarjejeniyar ba. Kasashe masu arzikin man fetur na kungiyar OPEC, ciki har da Najeriya, da farko sun yi kunnen kashi da kiraye-kirayen da kasashe sama da 100 suka yi na daukan tsauraran matakai kamar daina hako albakatun mai gaba daya.

Salisu Dahiru shi ne daraktan majalisar kula da sauyin yanayi ta Najeriya. Ya halarci zaman taron a Dubai a ranar Laraba.

Ya ce “Babu adalci da daidaito a cikin abin da aka kira matsayar neman kasashe masu tasowa ko kuma neman kasashen Afirka da hayakinsu ya kai kashi uku cikin 100 kawai su fara daina hako mai. Suna da wata boyayyar manufa. Su ne wadannan kasashen da ke kira kan wannan, Amurka da Tarayyar Turai da wasu ‘yan kadan. Wadannan albarkatun man suna da matukar muhimmanci ga kasashe masu tasowa don su dandani dadin ci gaba. Abin da a ko yaushe muke tsayuwa a kai shi ne mu tsarkake mai da iskar gas ta yadda za mu samu tsabtataccen makamashi.”

Masu suka sun ce fasahar tana da tsada, kuma wata dabara ce ta karkatar da hankalin kasashe daga ci gaba da samar da albarkatun mai.

Man fetur na samar da kashi 95% na kudaden shiga da Najeriya ke samu daga kudaden waje. Tarfa ya ce dole ne hukumomi su fara duba wasu wurare domin bunkasa tattalin arzikin Najeriya.

Ya ce “Akwai wuraren saka hannun jari da yawa a halin yanzu da ke kaiwa ga tattalin arzikin makamashi mai tsafta. Ga Najeriya, ba zamu ware kan mu ba. Duk da cewa da dainawa ko rage amfani da man fetur zai yi tasiri ga tattalin arziki. Amma yanzu lokaci ya yi da gwamnati za ta fara karkata zuwa wasu hanyoyin.”

A wani sharhi da ya rubuta wa gidan talabijin na CNN da aka wallafa a ranar Laraba, Shugaban Najeriya Bola Tinubu, ya ce Najeriya ta fara shirye-shiryen sauya sheka daga albarkatun mai, amma kasar na bukatar dala biliyan $10B a duk shekara har zuwa shekara 2060, domin cimma shirinta na sauya sheka.

Tinubu ya kuma soki lamirin kasashen da suka ci gaba na rashin cika alkawarin bai wa kasashe matalauta dala biliyan $100B, domin dakile illolin sauyin yanayi.

Duk da haka, masana sun ce yarjejeniyar COP28 za ta iya zama wani sauyi ga duniya idan aka samu kudirin siyasa da kudi, don cimma manufofin da a ka sa gaba.

Dandalin Mu Tattauna

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG