Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Muna Goyon Bayan Sabbin Takardun Naira - Shugaban EFCC


Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC
Abdulrasheed Bawa, shugaban hukumar EFCC

Hukumar yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya EFCC ta ce tana tare kai da fata da Babban Bankin Najeriya CBN, a kan sabbin takardun kudin Naira da za’a fara aiki da su a tsakiyar watan Disamba mai zuwa.

A hirarshi da Muryar Amurka, Shugaban Hukumar EFCC, Abdulrashid Bawa, ya ce yin haka yana da muhimmanci kwarai domin zai taimaka wajen sanin kudaden da ke na kwarai da wadanda ba na kwarai ba,

Bawa ya ce “yanzu sun zo a matsayinsu na kasa Najeriya wadanda kudaden da babban bankin ya ce yana da su ke zagayawa a Najeriya, kashi 85 cikin 100 na hannun mutane, inda kashi 15 cikin 100 ne kawai ke bankunan Najeriya, to ta wannan hali , ya ya zaka kawo tsarin kudi da zai duba sha’ani na kudade ya zamanto da cewa zai yi tasiri, ai ba zai yi tasiri ba.”

Ya kara da cewa, Dole ne CBN ta dauko wani mataki wanda za ta fara tun daga kasa da za ta rinka saka ido na wadannan abubuwa.“Wannan abun mun yi na’am da shi, zai taimaka mana wajen ayyukanmu, zai taimaka mana a abubuwa da yawa, nasara ba wai lallai a ganta yanzu ba, amma idan Allah ya so nan gaba kadan za’a ganta,” in ji shi.

Da yake amsa tambaya a kan cewa wasu na kallon kamar fargar jaji ce aka yi a yanzu, tunda dama masu ajiye irin wadannan kudade, kudaden kasar waje suke saya suna hidindimunsu na yau da kullum, yaya zaku tunkarin wannan bangaren shi ma ku karya lagon masu tattara irin wadannan kudaden kasar waje wadanda aka yi amfani da kudin haram aka tanade su, Bawa ya ce "Najeriya tana da tsari da kowane sati ta kan dauki kudade ta ba masu canjin (BDC), wannan yana daya daga cikin abubuwan da yasa akwai irin wadannan kudaden da ke ta zagayawa a Najeriya, yanzu an daina wannan, anfi wata shida ke nan da daina wannan.”

Ya kuma kara da cewa "kudaden da CBN ta ke bayarwa na BPA da PTA shima yana nan . Ya ce, suna basu shawara da cewa, su rika sawa mutane wadannan kudade ta hannun asusunsu da katuttukansu, don dai a rage irin wadannan abubuwa na dalar Amurka da ke zagayawa a nan, kuma ko da an ba mutum yana so ya canza Naira ne, mutane kuma suna zuwa suna karbar kuddaden tsaba ne. Don haka, a hankali a hankali idan Allah yaso za’a samu matsaya da masalaha kuma wadannan kudade ana amfani da su wajen sayan gidaje da sauransu."

Bawa ya ce daya daga cikin dokoki masu amfani da gwamnati ta kawo shi ne na kwarmata masu kudaden sata wanda ake bukata s‘yan Najeriya su taimaka da bayani, a nata bangaren kuma, hukuma za ta saya sunan wanda ya kwarmata labarin ta kuma yi mashi tukuici.

Saurari cikakkiyar hirar cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00

XS
SM
MD
LG