An ci gaba da fafutukar neman jagoranncin shugabancin majalisar tarayyar Najeriya ta goma a karshen makon da ya gabata bayan da jam’iyya mai ci ta ayyana wanda take so ya ja ragamar shugabancin Majalisar zabin zababen shugaban kasa Bola Ahmad Tinubu.
A wani sabon al’amari da ya kunno kai a gwagwarmayar neman shugabancin majalisar Tarayyar Najeriyar a ranar Asabar, mutane 4 da suke neman shugabancin majalisar sun fara tattaunawa kan yiwuwar kulla kawance gabanin bukin kaddamar da majalisar a ranar 13 ga watan Yuni na shekara ta 2023.
Jiga jigan wadanda suke neman shugabancin majalisar sun hada da Ahmad Idris Wase, wanda a halin yanzu yake rike da mukamin mataimakin kakakin majalisar kwamitin tarayya, sai kuma Aliyu Betara, wanda a yanzu shi ne shugaban kwamitin kudade, sai kuma Sada Soli da Sani Jaji; dukkaninsu sun gana da daren ranar Asabar a gidan daya daga cikin su dake Maitama a Abuja inda suka amince su yi aiki tare.
Wannan taron ya biyo bayan sa’o’i 24 da rahotanni su ka bayyana Tajudeen Abbas, daga jihar Kaduna, a matsayin zabin wadanda rahotanni suka bayyana da CABAL din Lagos, da kakakin majalisar mai baring ado Femi Gbajiabiamila yake jagoranta.
Wannan Al’amari na faruwa ne a daidai sa’adda aka samu rarrabuwar kawuna a tsakanin kungiyar ta majalisar wakilai akan zabin Tajudeen a matsayin wanda zababben shugaban kasa yake so ya ja ragamar shugabancin majalisar.
Rahottanin da jaridar Gurdian ta wallafa sun bayyana, cewar, wani makusancin Tinubu, kuma sakataren Kungiyar gangamin yakin neman zaben Tinubu James Faleke ya yi zargin Gbajiabamila da yada labaran da ba daidai ba.