Alkaluman da Jami’ar Johns Hopkins ta fitar, sun nuna cewa Amurka ce kasar da aka fi samun mace-mace sanadiyyar cutar coronavirus a duk fadin duniya.
A ranar Asabar, an samu tabbacin mutum 503,600 na dauke da cutar sannan mutum 18,860 sun mutu.
Hakan na nufin Amurka ta sha gaban Italiya a yawan wadanda suka mutu sanadiyyar coronavirus.
Adadin mace-mace a Italiyan ya kai 18,849 a ranar Asabar, kamar yadda kididdigar ta Johns Hopkins ta nuna.
Baya ga haka, Amurka ce har ila yau ta zama kasa ta farko da ta samu sama da mutum 2,000 da suka mutu a rana guda.
A ranar Juma’a Amurkan ta sanar da sabbin alkaluman mutanen da suka mutu wanda shi ne adadi mafi yawa da aka gani a duk fadin duniya tun bayan cutar barkewar cutar a China a watan Disambar bara.
New York ce jihar da aka fi samun mace-mace a Amurka inda gwamna Andrew Cuomo ya bayyana mutuwar mutum 783 a rana guda – adadin da ya kai jimullar sama da mutum 8,600.
Facebook Forum