Kamar yadda ba a rasa ji ba, an rantsar da Shugaban kasar Ghana Nana Addo Dankwa Akufo Addo na jam’iyyar NPP jiya Alhamis, a matsayin Shugaban kasa na Janhuriya ta 4 ta kasar Ghana a ginin Majalisar Dokokin kasar.
A bayaninsa bayan rantsarwar, Shugaban na Ghana, wanda ya gode ma al’ummar kasar baki daya tare da shan alwashin yin aiki ma kowa da kowa, sannan ya jinjina ma Kakakin Majalisar. Ya ce, “Ba tare da bata lokaci ba, zan taya babban aboki na, Honarabul Alban Sumana Kingsford Bagbin na jam’iyyar NDC murna saboda nada shi Kakakin Majalisa a Janhuriya ta 4.
Babban Alkalin kasar, Kwasi Anin-Yeboah ne ya rantsa da Shugaba Addo da Mataimakinsa Dakta Mahamudu Bawumia. Bukin rantsarwar ya zamu samu halartar shugabannin wasu kasashe ko kuma wakilansu. An dan samu jinkiri da matsala wajen shirya bukin saboda wata danbarwar da ta barke kan zaben shugabannin Majalisar da kuma batun rantsar da su da abin ya dau salon bangaranci da siyasa.
Wani abu kuma da ya fito fili ya kuma ja hankali shi ne yadda dukkan mambobin jam’iyyar NDC su ka kaurace ma bukin rantsar da Shugaban kasar saboda jaddada matsayinsu na cewa an tafka magudi a zaben.
Shugaba Addo ya yi kira ga Kakakin Majalisar, wanda dan wata jam’iyyar ce, da su hada kai tare don ciyar da kasar gaba. “Wannan ne karon farko a tsawon wannan Janhuriyar da Shugaban kasa zai yi aki tare da Kakakin Majalisa daga wata jam’iyya daban.”
Ga Ridwan Abbas da cikakken rahoton:
Karin bayani akan: Nana Akufo-Addo, John Dramani Mahama, NDC, da Ghana.