Sani ‘dan jarida daga jahar Nasarawa da Mr Stephen daga Jos sun bayyana irin tsaiko da aka samu da fatan wadanda suka ci zaben za su share wa al’umma hawaye.
Mafi yawan rumfunan zaben da muryar Amurka ta zagaya a cikin birnin Jos, an lura cewa jama’a sun fito kwansu da kwarkwatansu don kada kuri’a, duk da cewa a wasu wurare an sani rahotannin kaurace wa zaben saboda matsalolin rashin kai kayan aiki a kan lokaci.
Al’umma sun yi fatan shugabannin da za a zaba za su kawo sauyi mai inganci a rayuwarsu.
Zaben ya kai tsakar dare a wasu rumfunan zabe, inda jama’a suka jajirce su kada kuri’unsu a cikin daren.
A halin da ake ciki dai a yau lahadi da karfe goma sha biyun rana ne, hukumar zabe mai zaman kanta zata fara tattara kuri’u na zaben shugaban kasa da ‘yan majalisun tarayya.
Saurari rahoton Zainab Babaji: