Shugaban kungiyar kiristocin reshen jihar Kaduna, Rabaren Joseph John Hayab wanda ya yi jawabi a wani taron limaman coci-coci da kuma kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna ya ce akwai bukatar jami'an tsaro su tashi tsaye.
A baya dai hare-haren 'yan-bindiga a wasu sassan jihar Kaduna ya hana manoma da 'yan-kasuwa da dama sukuni.
Sai dai duk da samun sauki yanzu 'yan-bindigan sun sauya salo ta yadda suka kai hari a wani masallaci da Saya-Sayan karamar hukumar Ikara da kuma wata majami'a fadan Kamantan a Kudancin Kaduna.
Shugaban kungiyar kiristoci na jihar Kaduna, Rabaren Joseph John Hayab ya ce alkalumman rayukan da suka halaka na da ban tsoro.
Duk da yake taron limaman coci-coci ne kan tsaro, kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna CP Musa Garba ya ce masu kai hare-haren nan fa kowa ma kashewa suke ba tare da la'akkari da addini ko kabila ba.
Shi ma dai mai-magana da yawun majalisar koli ta harkokin addinin Musulunci, Malam Abdullahi Bayero, ya ce tunkarar 'yan-bindigan kawai don kare kai shi ne mafita ga al'umar Najeriya.
Kafin tashi taron tsara tsarin tsarkake tsaron dai sai kwamishinan 'yan-sandan jihar Kaduna ya tabbatarwa da mahalarta taron cewa 'yan-bindiga da sauran bata-gari ba za su sami sakat a lokacin shi ba saboda haka ya nema al'uma su baiwa rundunar yan-sandan hadin kai wajen fallasa taba-gari.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna