Wannan dai ya biyo bayan sabon harin da 'yan-bindiga su ka kai wa gidan wani malamin addinin kirista ne a fadan Kamantan da ke kudancin Kaduna kasa da mako guda bayan harin da aka kai wa wasu masallata a garin Saya-Saya a karamar hukumar Ikara.
Da farko dai 'yan-bindigan sun yi yunkurin shiga gidan malamin kiristan da ke Fadan Kamantan ne amma da abu ya gagara sai su ka cinna wa gidan wuta wadda ta yi sanadin rai guda. Kuma rundunar 'yan-sandan jahar Kaduna ta tabbatar da kai harin sannan ta ce ta dauki matakan gaggawa, inji mukaddashin mai-magana da yawun rundunar a Kaduna ASP Mansur Hassan.
Kungiyar kiristoci ta jahar Kaduna ta ce wannan sabon harin na da ban tsoro saboda haka Shugaban kungiyar Rabaren Joseph John Hayeb ya ce akwai bukatar gwamnati ta lura.
Ya kuma jaddada cewa matukar gwamnati ba ta dauki matakan gaggawa ba to dawowar hare-haren 'yan-bindigan zai maida hannun agogo baya saboda halin kuncin rayuwar da mutane ke ciki yanzu.
Da ma dai a ranar A;lhamis rundunar 'yan-sandan jahar Kaduna ta gurfanar da wasu 'yan-bindiga 13 da ta kama kuma ta ce ta hallaka wasu guda hudu sai dai kuma a daren ranar ne aka kai wannan sabon harin wanda wannan ne kuma ya sa ASP Mansur Hassan ya ce rundunar ta kara zage dantse.
Jahar Kaduna dai na cikin jahoshin Arewa maso yamman da hare-haren 'yan-bindiga su ka hana sukuni masamman a bara; sai dai kuma duk da samun sauki a farko-farkon wannan shekara, yanzu an fara samun hare-haren a jefi-jefi a wasu sassa.
Saurari rahoton:
Dandalin Mu Tattauna