Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo, ya ce har yanzu jami’an hukumar lafiya ta duniya (WHO) basu fito fili sun bayyana wa China laifinta na kin bada bayanan tushen coronavirus ba.
Babban jami'in a bangaren diflomasiyyar Amurka yana goyon bayan matakin da shugaba Donald Trump ya dauka na dakatar da ba hukumar tallafin kudade na tsawon kwanaki 60 zuwa casa’in.
Manazarta al’amuran lafiya a fadin duniya sun caccaki wannan mataki na Trump, kana sun bayyana cewa fiye da ko yaushe, a yanzu ne ayyukan hukumar WHO ke da matukar muhimmanci.
A yayin da annobar coronavirus ke ci gaba da gallabar mutane a duk fadin duniya, Mike Pompeo na ci gaba da caccakar jam’iyyar gurguzu ta China mai mulki akan yadda ta ki fitar da bayanai game da kwayar cutar, ya kuma caccaki hukumar WHO da laifin kin tsawata wa gwamnatin China.
Facebook Forum