Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ya Kamata Gwamnatin Najeriya Ta Kara Sa Ido Kan Hukumar Yaki Da Shan Kwayoyi - Masu Fafatuka Kan Miyagun Kwayoyi


Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi
Wasu daga cikin miyagun kwayoyi da hukumomi suka kwato a hannun masu safarar miyagun kwayoyi

Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da hukumar ta ce ta yi kame da yawa na wadanda ke dabi'ar, daidai lokacin da ake kara fadakarwa kan zagayowar ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya.

Hukumar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta Najeriya ta ce wahalar da ake samu wajen tattara hujjoji a kimiyyance, masu nuna tabbacin kwankwadar miyagun kwayoyin ga wadanda ake tuhuma idan aka gurfanar da su gaban kuliya, na ci gaba da zama babban cikas ga fafatukar da take yi.

Wannan na zuwa ne lokacin da hukumar ta ce ta yi kame da yawa na wadanda ke da hannu a wannan dabi'ar, daidai lokacin da ake kara fadakarwa kan zagayowar ranar yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi ta duniya.

'Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi a Niger
'Yan sanda sun kama miyagun kwayoyi a Niger

Najeriya ta kasance daya daga cikin kasashen duniya dake fafatuka wajen yaki da sha da safarar miyagun kwayoyi saboda illolin da suke haifarwa a cikin al'umma musamman ma wannan lokaci da rashin tsaro ya addabi jama'a.

Hukumar ta yaki da shan kwayoyin ta ce tsaye take wajen sauke nauyin da ya rataya a kanta kuma karkashin jagorancin shugabanta Muhammad Buba Marwa tana samun nasarori a jihohi daban daban.

A jihar Sakkwato kadai hukumar ta samu nasarar kame kayan mayen da nauyinsu ya kai kusan kilogram miliyan biyu, kuma ta kama wadanda take tuhuma da laifi da yawansu ya kai 247 daga watan Janairun 2022 zuwa yau.

Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyi
Hukumar Yaki Da Fataucin Miyagun Kwayoyi Ta Kama Wasu Dilloli Dauke Da Kwayoyi Na Daruruwan Miliyoyi

Sai dai kumandan hukumar a Sakkwato, Iro Adamu Muhammad, ya ce suna fuskantar kalubale idan suka gudanar da masu laifi gaban kuliya.

Duk da haka wasu ‘yan Najeriya na tsokaci akan kamen da hukumar ke yi. Da kuma tambaya kan me take yi da abubuwan da aka kama? Hukumar ta ce tana kona kayan da ta kama na maye domin barin su ba ya da amfani cikin al'umma.

Kumandan hukumar a Sakkwato ya ce sun ma tsara kona wasu kayan da suka kama a watan gobe.

Harwayau wasu jama'a kamar wani mai fafatuka akan miyagun kwayoyi, Nuraddeen Attajiri, na ganin ya kamata gwamnatin Najeriya ta kara sa ido ga hukumar yaki da shan kwayoyi, tare da kara samar wa hukumar ingantattun kayan aiki don kara azama ga aiki.

Hukumar dai ta ce duk kalubale da take fuskanta ba zasu sa tayi sanyi ba wajen gudanar da aikinta da yake tana da jajirtaccin shugabanni da ma'aikata, sai dai tana neman gudunmuwa daga kowa domin kara samar da al'umma tsarkaka daga sha ko fataucin kwayoyi.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
XS
SM
MD
LG