Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Mun Samu Gagarumar Nasara Wajen Yaki Da Miyagun Kwayoyi A Najeriya- Hukumar NDLEA


Hukumar Yaki Sha Da Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Najeriya, NDLEA
Hukumar Yaki Sha Da Safarar Miyagun Kwayoyi Ta Najeriya, NDLEA

Hukumar dake yaki da sha da fataucin miyagun kwayoyi a Najeriya NDLEA ta bayyana cewa, cikin watanni 22 da suka gabata hukumar ta yi nasarar kwato fiye da kwayoyin Tramadol miliyan dari da wasu  tarin haramtattun kwayoyi wadanda ke illata rayuwar matasa da cigaban Najeriya.

Shugaban hukumar ta NDLEA, Burgediya janar Buba Marwa ne ya bayyana hakan a yayin taron bikin karshen shekara ta 2022 inda aka karrama wasu daga cikin jami’an da suka nuna hazaka da jajircewa wajen gudanar da ayyukansu mabanbanta tare da kara musu girma a hukumar, inda ya ce an yi nasarar kama masu safarar miyagun kwayoyi dubu 23,907 ciki har da gungun masu sayar da kwayoyi su 29.

Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa
Shugaban NDLEA, Janar Buba Marwa

Kazalika an kama fiye da ton dubu 5,500 na haramtattun kwayoyi wadanda idan aka hada har da kudaden da aka kama jimillar su zai kai sama da Naira biliyan 450.

Burgediya janar Buba Marwa dai ya danganta wannan nasara da hukumarsa ta samu bisa ga gudumawar da shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bayar ga aikin hukumar na dakile yaduwar miyagun kwayoyi a kasar da kuma jajircewa jami’an hukumar.

A hirar shi da Muryar Amurka, Usman Aliyu Wada babban Komanda na hukumar a filin tashi da saukar jiragen sama na Murtala Muhammad dake jihar legas, kuma daya daga cikin jami’an da aka karrama ya bayyana farin cikinsa tare da kari kan cewa wannan karramawa da aka yi masa za ta kara masa kaimi wajen rubanya kokarin da suke a yayin gudanar da ayyukansu a gaba.

Shima DCGM Sani Ibrahim Sani shugaban sashin gudanarwa da harkokin kudi a hukumar ya ce samar musu da kayyakin aiki da kuma basu horo akai akai da kula da walwalarsu ya sa aka kai ga cimma wadannan nasarori da aka samu a yanzu.

Hukumar dai ta jaddada niyarta na kara zage dantse don yaki da miyagun kwayoyi a Najeriya inda ta ce ba sani ba sabo ga duk wanda aka kama da laifi a yakin da ta sa a gaba

Saurari rahoton cikin sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:15 0:00

XS
SM
MD
LG